30 Maris 2022 - 14:47
Isra’ila : An Kashe Mutum 5 A Wasu Jerin Hare hare Kusa Da Tel Aviv

Rahotanni daga Isra’ila na cewa akalla mutane biyar ne aka kashe jiya talata a wasu hare-hare na masu dauke da makamai a kusa da birnin Tel Aviv.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Harin na yankin Bnei Brak, na yahudawa masu tsattsauran ra'ayi na Orthodox shi ne hari irinsa na uku a cikin mako guda a Isra’ila, inda mutum 11 suka mutu a garuruwa uku daban-daban.

Bayanai sun ce Firaministan Isra'ilar Naftali Bennett ya gana da manyan jami'an tsaro da yammacin jiya bayan hare-haren.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas yayi Allah wadai da tashin hankalin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kisan gillar da ake yi na kara dagula al’amura yayin da dukkanmu muke kokarin ganin an samu kwanciyar hankali.

342/